Assalamu Alaikum
Sako daga NASSCO, SOCU – UPDATE ON NATIONAL SOCIAL REGISTER AND NATIONAL IDENTIFICATION NUMBER INTEGRATION EXERCISE
Ana sanar da wadanda sunansu yake cikin Social Register cewa za’azo ayi update tare da hada bayanan mutane da katin dan Kasa kowane lokachi daga yanzu Domin amfana da Tallafin 75,000 da cin gajiyar sauran tallafin da ka iya zuwa Kai tsaye daga gwamnatin Tarayya ga ko wane Dan kasa Wanda yake cikin National Social Register. Dangane da haka ake sanar da mutane cewa duk wanda bashi da katin dan Kasa (NIN) ya hanzarta yaje yayi, ya kuma Bude asusun ajiya a Bankin da Yake so. *NASSCO, NIMC, SOCU* zata turo ma’aikata gida gida bisa Jagoranchi Magaddai da Masu Unguwanni domin suyi updating na Social Register a hada bayanan mutane da Katin Dan kasa da kuma lambar asusun ajiya na Banki.
Ana kammala aikin da yardar Allah duk tallafin da gwamnati zata bayar kawai za’a sameshine Kai tsaye ta asusun ajiya na banki
Don Allah a sanar da Al’umma yadda yakamata
Nagode.