NYIF UPDATE:::
An Fara Aiki Gadan Gadan Ga Wadanda suka Nemi Wannan shiri, An sami jinkirin Aikace Aikacensane Sakamakon bibiyar yadda shirin yayi nasara a baya da yadda zaiyi a yanzu.
A baya Shirin ya kasance akan matasa masu shekara daga 18 zuwa 35 Inda dubban mutane masu CAC suka amfana kudi daga kan miliyan uku zuwa kasa.
Yayinda ita kuma Wannan Gwamnatin ta bada dama a sake yin Applyin na wannan shirin a watanni baya, Inda aka ware matasa maza da mata masu shekara daga 18 zuwa 40
Masu CAC an basu damar su nemi daga miliyan daya zuwa goma, Yayinda individial kuma zasu nemi kudi daga dubu dari zuwa miliyan daya.
Abin Nufi Masu CAC bashi kudinsu zai kasance, Amma kudin zasu fara daga miliyan daya zuwa sama, Yayinda Wadanda za’a bawa kyauta kudinsu zai kama daga dubu dari zuwa sama.
An cike shirin kamar yadda nafada a baya, Bawai yanzu ake cike shiba, Kuma duk Wanda ya cike a baya, Wani bangare ya cike na shirin bai gama komai ba,
Nan gaba zaka iya ganin sako ta email ko text SMS na waya domin kara saka bayananka da sauran ka’idoji.
Shi Wannan shiri mai dogon zangone, An tsarashi tin a Gwamnatin Buhari data gabata kuma anaso yakai shekara ta 2030 idan ALLAH ya kaimu, Inda akeso shirin ya taka rawa wajan fitar da matasa daga talauci da rashin aikin yi.